20 Oktoba 2020 - 13:43
Shugaban ‘Yan Adawar Kasar guinea Diallo Ya Shelanta Kansa A Matsayin Wanda Ya Ci Zabe

Shugaban ‘Yan Adawar Kasar guinea Diallo Ya Shelanta Kansa A Matsayin Wanda Ya Ci Zabe

ABNA24 : A jiya Litinin ne Diallo ya bayyana cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a shekaran jiya Litinin inda ya kara da shugaba Alpha Conde.

Diallo wanda ya gabatar da taron manema labaru a birnin Conakry ya ce; Duk da magudin da aka yi shi ne ya lashe zaben.

Har ila yau dan takarar bangaren hamayyar ya yi kira ga al’ummar kasar da su kasance cikin sa ido, tare da yin alkawalin kare tsarin demokradiyyar kasar.

Sai dai bangaren gwamantin kasar ya yi watsi da sanarwar jagoran ‘yan hamayyar tare da cewa; ba aikin daidaikun mutane ba ne su shelanta kansu a mastayin wadanda su ka ci nasara.

342/